Tarihin Sardauna


Yadda Muka Yi Da Nzeogeu Bayan Ya Kashe Sardauns, Cewar Marigayi Sheik Abubakar Gumi

Daga Ghaddafi Albashir

Kamar karfe hudu na asuba ranar Juma'a aka bugo mun waya bayan na dauka sai na ji ministan ilimi na Arewa Alhaji Isa Kaita, ya ce mun sojoji fa sun yi juyin mulki, har an kai wa gidan Sardauna hari kamar yadda ya ce mun duk manyan jami'an gwamnati sun buya. Ya ce mun, ya yi magana da Hassan Katsina, amma Hassan dai a lokacin ya ce mai babu abun da zai iya yi. Hassan ya ce mai a wannan lokacin ma yana ganawa ne da bujirarrun sojojin. Isa Kaita, ya ce mun ya kamata ni inje gidan Sardauna in ganewa idanuna abunda ke faruwa.

Bayan na kintsa na yi sallar subahi, na kuma kama hanya na nufi gidan Sardauna, naje na iske gidan anyi kacha-kacha, da shi alamu kuma sunnuna anyi amfani da manyan makamai wurin lalata gidan. Har lokacin da na Isa gidan hayakine a turnuke. Sai wasu tsirarun sojoji ne a tsaye da bindigogi a hannunsu, ko ina tsit. Haka na wucesu na kutsa kaina cikin gidan, ina shiga naci Karo da gawar firimiya a kwance a filin da ake aje motoci na gidan.

Nan danan nace a dauki gawar a kaita gidan Sarkin Musulmi, dake unguwar Sarki, Sardauna, da shi da uwargidansa Hafsat aka kashesu.

Bayan mun gama kintsashi, rana Kuma ta fara dagowa nine na Sallaci duka gawauwakin. Ina sane Kuma da cewa anyi babban rashi-rashin Kuma dai nan kurkusa abune mawuyace a samu kamarsa.

Akan hanyata ta dawowa gida daga wurin jana'izar Sadauna, na wuce gun-gun mutane sun taru sunata alhinin abunda ya faru. Bayan na samu natsuwa abubuwa sun koma kamar yadda suke ranar komawa aiki na shirya kamar kullun na tafi wurin aikina. Ina cikin ofishina da safe sai ga motar sojoji, cike da sojoji, ta shigo harabar wurin aikina. Wasu daga cikin sojojin suka sauko a mota suka tambayi inda ofishina yake. Bayan sun shigo ofishina sukai mun gaisuwa irinta ta girmamawa, suka ce anturone su tafi dani maigidansu Nzeogwu, yana son ganina.

Kuma zan shiga motarsu ne tilas su tafi dani amma zan iyasa wani cikin ma'aikatana ya bimu a baya shi sai ya dawo dani. Natashi na bisu banyi musu ba na umarci direbana ya bini da mota bayan mungama ganawa ya dawo dani. Bayan mun isa barikin sojan inda shi Nzeogwu yake. Na ga sojoji da yawa suna gadin barikin kowane soja sabe yake da bindigarsa.

Bayan mun yi fakin muka sauko daga mota muka shiga cikin ofishin, cikinmu ba wanda yaima wani magana tsakanina da wayannan sojojin. Bayan sun kaini inda Nzeogwu yake, ya kuma tare ni cikin fara'arsa na kuma zauna akan kujera, sai ya fara magana cikin tattausar murya.

Abunda yake son sani shine ina muka boye makaman da muka siyo? Wannan tambayar tasa ta ba ni matukar mamaki, na ga ni dai a rayuwata ban ma taba ganin Nzeogwu ba, ban kuma taba wata alakar ta rayuwa da shi ba. Ni a tunani na ma shi ne ya kira ni ya yi mun ta'aziyar rashin Sardauna, da na yi ko kuma ya nuna dana saninsa akan abunda ya aikata. Dama ban yi tsammanin kalamai na ban hakuri daga gare shi ko nadama akan abunda ya aikata tunda na lura yana al'afari da abunda ya aikata.

Abunda kuma ya kara bani mamaki wanda suka sabi makamai suka yi Juyin mulki wai a lokacin ne suke kokarin tattara hujjojinsu ko kuma dalilan hambarar da wannan gwamnatin. 

Sai nagama kafin in ba shi amsar tambayarsa yakamata in nemi karin bayani daga gare shi. Sai ya ce mun a irin labaran da ya samu an ce mai mun siyo makamai masu tarin yawa mun shigo da su cikin kasa, Kuma mun siyo makaman ne daga kasashen gabas ta tsakiya. Kuma niyar mu ita ce mu kaddamar da jahadi akan wadanda ba musulmai ba, shi ya sa yake so na gaya mai inda muka boye makaman.

Lokacin da na zo ba shi amsar tambayarsa na tabbatar mai cewar ni a wurinsa ma na fara jin wannan maganar, na kuma tabbatar ina magana ne a matsayina na mashawarcin Sardauna, akan harkokin da suka shafi addinin Musulunci. Kuma na tabbatar mai da cewa Sardauna, bai taba zuwa wata kasar Larabawa a matsayinsa na firimiya ba tare da ni ba. Kuma ban taba  ji ya yi maganan makamai ba a wata kasar larabawa, balle ma har mu siyo mu shigo da su Nijeriya, da sunan wai zamu yaki wadanda ba musulmai ba.